Samame Gidan Alƙalin Babbar Kotu Yunƙurin Kisa Ne – Kotun Koli

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Hukumar dake kula da kotun koli a ranar Talata ta yi martani kan harin da jami’an tsaro suka kai gida mai shari’a Mary Odili a ranar Juma’a da ta gabata.

A wata takardar da daraktan yada labarai, Festus Akande, na kotun kolin ya fitar, ya ce kutsen ya fi kama da yunkurin kashe alkalin ko kuma nakasa ta.

An ruwaito cewa, an kai hari ne da sunan an je bincike wanda kuma takardar izinin binciken ba ta da tushe kuma cike ta ke da kauyanci tare da abun kunya.

“Mun samu labarin wani irin hari da aka kai gidan daya daga cikin manyan alkalan kotun koli, Mai shari’a Mary Peter Odili a ranar Juma’a, 29 ga watan Oktoba ta wata hanya mara kyau.

“Wasu ne da ake zargin jami’an tsaro ne dauke da makamai wadanda ke wakiltar wasu cibiyoyin gwamnati suka kai harin da alama sun je kashe ta ko nakasa ta ne inda suka boye da sunan zuwa bincike gidan.

“Mun yi matukar takaici kuma an mayar da mu baya ta hanyar wannan abin kauyancin da na kunya wanda aka yi wa jami’ar shari’a wacce ta kwashe shekaru masu muhimmanci na rayuwar ta ta na bauta wa kasar ta.”

Labarai Makamanta