Sama Jannati: Saudiyya Za Ta Tura Mace Ta Farko Sararin Samaniya

Hukumar kula da sararin samaniya ta Saudiyya ta ƙaddamar da shirin sama jannati a karon farko da ya haɗa da aika mace ta farko ƴar ƙasar zuwa sararin samaniya a 2023.

Shirin zai mayar da hankali ne wajen horar da ƙwararru ƴan asalin Saudiyya don su yi tafiya mai nisan zango da mai gajeren zango a jirgin sama jannati zuwa sarrain samaniyar.

Shirin zai bai wa ƴan sama jannati Saudiyya damar aiwatar da binciken kimiyya don ci gaban ɗan adam a ɓangarorin da suka fi muhimmanci kamar lafiya da ci gaba mai ɗorewa da kuma fasahar sararin samaniya.Shirin Sama Jannatin na Saudiyya, wanda yana daga cikin burukan da masarutar ke son cimma a shekarar 2030, zai aika ƴan sama jannatin ƙasar don kyautata rayuwar mutane.

Ɗaya daga cikin ƴan sama jannatin mace ce ƴar asalin Saudiyyan, wadda tafiyarta za ta zama wani abu na tarihi da ba a taɓa gani ba a masarutar.A watanni masu zuwa Saudiyya za ta ƙaddamar da tsare-tsarenta na zuwa sararin samaniya, da suka haɗa da shirin yi wa al’umma hidima daga can.

Labarai Makamanta