Sama Da Yara Miliyan 15 Na Fuskantar Barazanar Yunwa A Najeriya – UNICEF

Asusun tallafawa kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya yi gargadin cewa kananan yara miliyan 14 da dubu 700 a Najeriya galibinsu ‘yan kasa da shekaru 5 da haihuwa na cikin hadarin kamuwa da cutar Tamowa wadda karancin abinci me gina jiki ke haddasawa.

UNICEF ta bayyana cewa idan har ba a dauki matakan da suka kamata ba, a shekarar da muke shirin ban kwana da ita, yara miliyan 13 za su fuskanci cutar tamowa yayinda wasu miliyan 1 da dubu 700 kuma za su fuskanci matsananciyar cutar ta Tamowa galibi a yankin arewacin Najeriya.

Asusun na UNICEF ya ce abin takaici ne yadda alkaluma ke nuna mutuwar kananan yara 100 ‘yan kasa da shekaru 5 da haihuwa duk bayan sa’a daya a Najeriya, yayin da wasu yaran na daban miliyan 12 ke cikin halin matsanancin rashin abinci.

Shugabar sashen abinci mai gina jiki ta UNICEF a Najeriya Nemat Hajeebhoy, ta ce yara a Najeriya na halin tsananin bukatar abinci mai gina jiki lura da yanayin da kasar ke ciki na tabarbarewar tattalin arzki da ya sanya iyalai gaza sabun isasshen abinci.

A cewar jami’ar matsaloli masu alaka da ambaliyar ruwa da ta lallata tarin amfanin gona a sassan Najeriya na shirin sake tsananta karuwar yaran da ke fama da wannan cuta ta rashin isasshen abinci mai jiki wato cutar yunwa ko kuma Tamowa.

UNICEF ta ce idan har gwamnatoci da sauran wadanda abin ya shafa basu dauki matakan da suka kamata ba, rayuwar kananan yaran masu fama da yunwa na cikin hadarin gaske, kari kan miliyoyin yaran da yanzu haka ke fama da cutar ta Tamowa.

Labarai Makamanta