Sama Da ‘Yan Najeriya Miliyan 25 Na Fama Da Matsananciyar Yunwa – Bincike


Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar sama da ‘yan Najeriya miliyan 25 ne ke fama da yunwa, yayin da mutane miliyan 9.3 ke fama da matsanancin karancin abinci, dai-dai lokacin da kasar kef ama da tashen-tashen hankula na masu dauke da makamai.

A cewar Farfesa Kola Matthew Anigo, babban jami’in kula da harkokin ilimi da bincike kan bunkasa abinci mai gina jiki a Najeriya, kasar na cikin mawuyacin hali da ta bukatar agajin gaggawa.

Farfesan ya bayyana haka ne a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun, a lokacin da yake gabatar da jawabi a taron shekara-shekara na kungiyar karo na 52.

Ya ce Najeriya ce ta daya a Afirka sannan ta biyu a duniya a jadawalin yara masu fama da cutar tamowa.

Anigo ya ce rashin tsaro da ake fama da shi a kasar yana yin babbar barazana ga Najeriya ta cimma burin samar da abinci mai gina jiki ga yara nan da shekarar 2025.

Masanin ya ce, ayyukan fashi, ta’addanci da kuma garkuwa da mutane sun taimaka wajen rashin wadataccen abinci, yana mai cewa Najeriya ba za ta iya samun wadatar abinci ba idan har ba a magance matsalar rashin tsaro ba.

Akwai bukatar a sauya tsarin noma da tsarin samar da abinci su kasance a matsayin manyan hanyoyin bunkasar tattalin arziki, amma dai-dai da girman matsalolin abinci mai gina jiki.

Labarai Makamanta