Sama Da ‘Yan Najeriya Dubu 17,000 Aka Kashe A Shekarar Bara – Rahoto

Wani rahoto da wani kamfani mai nazari kan harkokin tsaro ya fitar ya nuna cewa fiye da mutum 17,000 ne aka kashe a Najeriya, sanadiyar tashe-tashen hankula a shekara ta 2020 da kuma 2021 a sassan kasar.

Kamfanin SBM Intelligence ya alakanta kashe-kashen da hare-haren Boko Haram da na ‘yan bindiga da rikicin Fulani da manoma da garkuwa da mutane don neman kudin fansa da kuma fadace-fadacen kungiyoyin asiri.

Rahotan da kamfanin na SBM Intelligence mai bibiya da sharhi kan harkokin tsaro a Najeriya ya fitar yau, ya ce ya tattaro bayanan ne daga rahotannin wasu kafofin watsa labarai a kasar.

Rahoton ya ce mutum 7,063 aka hallaka a 2020 sakamakon rikicin Boko Haram da kuma na ‘yan bindiga, sannan a 2021 kuma aka kashe mutum 10,366, wato a kullum kenan ana kashe akalla mutum 28.

Labarai Makamanta