Rahoton dake shigo mana daga birnin Khartum na kasar Sudan na bayyana cewar Hukumomi a kasar ta Sudan sun ce yawan mutanen da suka mutu a rikicin ƙabilanci da ake yi a kudancin kasar tsakanin Hausawa da ‘yan kabilar Berta ya ƙaru zuwa 200.
Wani shugaban al’umma a Jihar Blue Nile ya ce an yi kashe-kashen ne a kauyuwa uku, inda ya yi kira ga kungiyoyin agaji da su taimaka wajen binne gawarwakin wadanda suka rasu.
Rahotanni na cewa rikici tsakanin Hausawa da Berta ya ɓarke ne kan gonaki.
A ranar Juma’a aka sanya dokar ta-ɓaci ta tsawon kwana 30 a fadin jihar ta Blue Nile.
You must log in to post a comment.