Sama Da Kashi Goma Na ‘Yan Najeriya Mashaya Ne – Bincike

Likitan kwakwalwa kuma babban jami’i a asibitin masu tabin hankali na Maiduguri, babban birnin jihar Borno, Dr Ibrahim Abdullahi Wakawa, ya bayyana cewa a cikin shekarar da ta gabata a Najeriya an gudanar da wani bincike da ya nuna cewa kashi 14 cikin dari na al’ummar Najeriya su na ta’ammali da miyagun kwayoyin da ke gusher da hankalin mutane, wanda hakan na nufin a duk daya daga cikin ‘dan Najeriya shida za a iya samun mai amfani da kwaya.

A jihar Borno kuwa binciken ya nuna cewa kusan 10 cikin dari, wato kowane mutum daya daga cikin 100 ya na amfani da miyagun kwayoyi. Hakan ya sake muni ne sanadiyar wannan rikici da a ka samu a wannan yankin, ya sa mutane da yawa sun samu kawukansu cikin mawuyacin rayuwa da ya ta’azzara su suke amfani da miyagun kwayoyi,idan aka duba shekarun da suka gabata da wuya kaga mata na ta’ammali da miyagun kwayoyi amma yanzu za ka ga mata na shaye-shayen miyagun kwayoyi, India binciken ya nuna cewa mata kashi shida cikin dari suna shan miyagun kwayoyi.

Dr Ibrahim Abdullahi Wakawa, ya kara da cewa “binciken ga nuna cewa matasa masu shekaru goma sha biyar zuwa hamsin ne, su ka fi ta’ammali da miyagun kwayoyin. Abune mai muhimmanci a rinka wayar da kan matasa akan illolin amfani da miyagun kwayoyi saboda idan aka duba sosai za a ga cewa duk kan wasu tamuran yau da kullum matasa ne suke tafiyar da shi.

“Yawancin mutanen da suke amfani da wannan miyagun kwayoyin mutane ne da a shekarun baya suke da abin hannu, su na zama a gidajen su kuma rayuwa tana tafiya yadda ake so amma sanadiyar wannan rikici na Boko Haram, to idan ba mutum bane yayi tawakkali ko yayi hakuri da yadda ya samu kansa ba yana wuya yaci gaba da rayuwa a cikin mawuyacin halin da bai saba ba.

“Wasu suna amfani da miyagun kwayoyin ne domin su kwantar da hankalin su ko kuma su manta da abubuwan da ya faru da su. Sannan a wajen da ‘yan gudun hijira su ke rayuwa ana samun wasu mutane da su ke zama dillalen kwayar, inda su ke kawo ta cikin mutane suna sayar wa anan ma ana samun wasu su fada cikin wannan halin.

“Canjin yana yi shine ya sanya Mata amfani da miyagun kwayoyi saboda a da can baya a nan Arewa Namiji ma idan ka gansa yana shan kwaya abin mamaki ne, amma yanzu za kaga kowa da kowa abin ya zama ruwan dare. Kuma babbar matsalar shine kafar sada zumunta da kuma yawan kallace-kallacen fina-finai suna taimakawa sosai.”

Related posts