Lokacin da al’ummar Duniya baki ɗaya ke murnar zagayowar ranar sallah babba, Shugaban Kamfanin ATAR Communication masu gidajen Talabijin da Rediyo na Liberty da Jaridun Muryar ‘Yanci da Voice Of Liberty, Kamfanin da ke sahun gaba a Najeriya wajen yada labarai, na taya dukkanin musulmi murna da wannan babbar rana ta sallah.
Tijjani Ramalan ya bayyana godiyarshi ga Allah da ya rayamu da ya yi har muka shaida ganin wannan rana ta sallah a wannan shekara, wadda ta zo da manyan ƙalubale ga jama’a da harkokin kasuwanci.
“Duk da kalubalen da cutar CORONA ta jefa jama’a da matsalar tattalin arziki, Kafafen yaɗa labaran Liberty zata cigaba da ilimantarwa da wayar da kan miliyoyin jama’a a faɗin tarayyar Nijeriya, Afirka dama duniya baki ɗaya, da ingantattu kuma sahihan labarai”.
“Muna amfani da wannan dama wajen sanar da jama’a cewa bisa ga rangwame da kwamitin yaki da cutar CORONA na fadar Shugaban ƙasa ya bayar akan wayar da kan jama’a dangane da cutar, da kuma albarkacin wannan rana ta babbar Sallah, mun zaftare farashin tallace tallacen mu da kaso 50, ga gwamnatoci da ɗaidaikun jama’a na tsawon watanni Uku.
Kamfanin Liberty zai cigaba da kawo muku shirye shirye da dama domin amfanar da al’umma baki ɗaya.
Muna godiya ga dimbin masu sauraron mu bisa ga juriya da jimirin kasancewa da mu a koda yaushe.
Muna godiya da fatan za’a cigaba da gudanar da bukukuwan sallah lafiya.
You must log in to post a comment.