SALLAH: An Shawarci Musulmi Kar Su Manta Darussan Ramadan – Ramalan

A daidai lokacin da al’ummar Musulmi a faɗin duniya ke gudanar da bukukuwan karamar Sallah, Shugaban Kamfanin ATAR Communication mamallakan Gidajen Talabijin da Rediyo na Liberty Alhaji Dr Ahmad Tijjani Ramalan, ya bukaci al’umma da kar su manta darussan da suka koya a yayin ibadar watan azumin Ramadan.

Ramalan ya bayyana hakan ne a cikin sakon barka da Sallah da ya aikewa jama’ar Musulmi na fatan kammala azumin Ramadan lafiya da bikin Sallah karama.

Sannan ya yi addu’a Allah ya amshi ibadun da Musulmi suka yi da sauran ayyukan alheri a yayin ibadar watan azumin Ramadan.

Lokacin da ya ke kira ga jama’a na cigaba da kulawa wajen kare kai daga cutar Covid 19 Ramalan ya kuma bukace su da yin taimako musanman ga masu ƙaramin karfi a yayin bukukuwan sallah domin su mori shagalin bikin sallah.

Ya bayyana cewar bikin sallah ƙarama na bayar da dama ga iyalai da makwabta da kuma abokai su taru wuri guda wajen addu’o’i da ci tare da bayar da kyaututtuka.

“Ina kira ga jama’a da cewa kada su manta bin dokokin kare kai daga cutar Covid 19. Bayan aikata hakan kar kuma a mance da taimakon jama’a marasa karfi, ya zamana mu kusance su ta yadda su ma zasu shaida cewar ana bukukuwan sallah”.

“A yayin da a yau muke gudanar da bukukuwan sallah kada mu manta da darussan da muka koya a yayin ibadar watan azumin Ramadan, mu cigaba da bin karantarwar wata mai tsarki. Ina amfani da wannan dama wajen kiran dukkanin ‘yan Najeriya Musulmi da wadanda ba musulmi ba suyi amfani da wannan lokaci wajen gudanar da addu’o’i domin samun zaman lafiya da tsaro a Najeriya.

“Ina kuma amfani da wannan dama wajen godiya ga dukkanin wadanda suka ɗauki nauyin tafsiran azumin bana da sauran shirye-shiryen addini, kuma ina godiya ga dimbin masu saurarar mu ta kafafen Rediyo da Talabijin da kafofin sada zumunta gaba ɗaya.

“Muna kara kira na samun goyon baya da fahimtar juna domin samun damar cika alkawarrun da muka ɗauka na kawo muku sabbin shirye shirye cikin harshen Hausa da turanci, labarai da al’amuran yau da kullum a babbar tashar mu ta Talabijin na Liberty dake birnin tarayya Abuja da sauran kananan tashoshin mu na FM dake Abuja, Kaduna da Kano a lokacin bukukuwan sallah, wanda zasu fara a makon gobe Litinin 17 ga watan Mayun 2021 a shirinmu mai farin jini dake zo muku da safe na “TAMBARI”

Labarai Makamanta