Sakon Tallafin Tinubu Na Raba Kudi Ga ‘Yan Najeriya Ba Gaskiya Ba Ne – Kwamitin Neman Zabe


Wata sanarwa da tawagar yaƙin neman zaɓen Tinubu ta fitar ta ce saƙon da ake yaɗawa na ƙarya ne kuma ba daga wurinsu ya fito ba.

“Muna tabbatar da wannan saƙon na ƙarya ne saboda ba daga wajenmu ya fito ba,” a cewar Festus Keyamo kakakin tawagar kamfe ɗin Tinubu/Shettima kuma Ƙaramin Ministan Ƙwadago na Najeriya.

Mista Keyamo ya zargi jam’iyyun adawa da “yunƙurin tura saƙonni marasa kan-gado da zimmar samun ƙuri’un ‘yan Najeriya”.

A ranar Laraba Bola Tinubu ya faɗa wa BBC cikin wata hira cewa tabbas shi mai kuɗi ne, duk da cewa wasu na yi masa hassada.

“Ba na gudun a ce ni mai kuɗi ne, amma dai wasu na yi min hassada game da dukiyata,” in ji shi.

Tinubu mai shekara 70 ya kuma bayyana cewa tun da ya sauka daga gwamnan Legas a shekarar 2007 bai sake riƙe muƙami ba ko kuma kwangilar gwamnati.

Kamar yadda ta yi a zaɓukan 2015 da 2019, wannan karon ma jam’iyyar APC mai mulki na neman tallafin kuɗin yaƙin neman zaɓe daga ‘yan Najeriya.

Magoya bayan jam’iyyar sun wallafa saƙonnin neman taimakon sau da dama a shafukansu na sada zumunta, cikinsu har da Bashir Ahmad – mataimaki na musamman ga Shugaba Buhari kan kafofin sada zumunta.

Kamfe ɗin Tinubu/Shettima ta ƙirƙiri shafin neman taimakon ne a dandalin blessmi, inda ake neman mutane su tura kuɗi ta wani asusun banki.

“Ku tallafa wa kamfe ɗinmu don taimakawa wajen cimma muradanmu kan ƙasarmu mai daraja,” a cewar saƙon da ke kan shafin.

Zuwa yanzu babu bayanan adadin kuɗin da suka tara na tallafin amma za a ci gaba da karɓa har nan da kwana 76.

Labarai Makamanta