Sakon Sallah: Shugaban LIBERTY Talabijin Ya Yi Kiran A Sanya Kasa Cikin Addu’a

Shugaban Kamfanin ATAR communications mamallakan liberty TV, liberty radio da jaridun yanar gizo na muryar yanci da voice of liberty, Dr Ahmed Tijjani Ramalan ya bukaci daukacin al’umar musulmi da suyi anfani da lokacin shagulgulan sallah wurin yiwa Najeriya addu’ar samun dawwamanmen zaman lafiya da hadin kan kasa baki daya.

Dr Ramalan ya bayyana hakan ne a sakon barka da sallar da ya fitar inda ya bukaci daukacin al’umar Najeriya da su hada kai wurin sadaukar da ibadun su Wurin addu’ar kawo karshen matsalar rashin tsaron da ya addabi kasar mu saboda tsaron kasa aiki ne daya rataya akan kowani ‘dan kasa.

Daga karshe yayi addu’ar Allah ya kawo wa najeriya zaman lafya da Kuma fatan za ai shagulgulan babban sallar Layya na wannan shekarar lafiya

Labarai Makamanta