SAKON SALLAH: MU RUNGUMI AKIDAR ZAMAN LAFIYA DA JUNA – OKOROCHA

Tsohon Gwamnan Jihar Imo kuma Sanata mai wakiltar mazaɓar Imo ta Yamma a majalisar Dattawa Sanata Owelle Anayo Rochas Okorocha, ya taya al’ummar musulmi murnar zagayowar ranar bikin Sallah babba, tare da yin kira a garesu da sanya kasa cikin addu’o’i a yayin shagulgulan bikin wannan rana.

“A madadin ni kaina da iyalina ina yi wa jama’ar Musulmin Najeriya da duniya gaba daya murnar ranar Sallah babba ina mai cewa “Barka Da Sallah”.

Tabbas Najeriya kasarmu ce ta gado ba mu da kasar da ta fita a duniya, saboda haka mu haɗa hannu mu kawar da dukkanin bambance bambancen dake tsakanin mu, mu taru mu gina Najeriya.

Nagode da fatan za a cigaba da gudanar da bukukuwan sallah Lafiya.

Labarai Makamanta