Sakon Sallah: Gwamnan Bauchi Ya Yi Kiran A Yi Koyi Da Annabi SAW

Gwamnan Bala Abdulkadir Mohammed na Jihar Bauchi, ya bayyana, Biyayya tare da sadaukar wa irin ta Annabi Ibrahim a mazaunin mizani ta kololowa da kuma cewa abar koyi ce ga al’ummar Musulmin duniya.

Gwamnan ya fadi haka ne a cikin sakon sa na Sallar Layya ga Jama’ar Bauchi da ma sauran Musulmin duniya baki daya

Kana ya shawarci musulmai suyi hangen nesa da tunani mai zurfi kan ayyukan da suka aikata na shekarar baya, domin gyara abubuwa da zasu zo maso a shekaru ma su zuwa.

Ya bayyana cewar, addinin musulumci yana karanta da biyayya da sadaukar da kai ga Allahu Subahanahu Wata’ala ne, da kuma samar da zaman lafiya tsakanin musulmai a dukkan tsawon rayuwar al’umma.

Bala ya kara da cewa, “Alkur’ani mai tsarki ya yi umarni wa dukkan musulmi da su rika bayar da sadaka daga cikin abin da Allah ya hore masu. kuma mutum zai aikata haka ne ba tare da bibiyar addini, kabila ko siyasar wani ba”.

Gwamnan ya kuma nemi musulmi su yi amfani da wannan dama domin karfafa zumunci tsakaninsu, da fito da wadansu hanyoyi na alaka ko sabunta zumuncin da hadin kai da kuma bukatar yafewa juna, tare da mutunta al’umma baki daya.

“Mu cigaba da yin addu’o’in zaman lafiya a jihar mu da addu’o’i na fatar samun wadataccen ruwan sama da damina mai albarka a jihar nan da ma kasa baki daya.” ya fada.

Bala, ya sake cewa, aniyar gwamnatin su na yiwa jama’a aiki tukuru domin kai jihar Bauchi ga tudun mun tsira, har’ila yau, “Muna matukar kokarin samar da ababen more rayuwa, tare da inganta su, bayar da ilimi, kiwon lafiya, karfafa matasa da bukkasa ayyukan gona”.

“Muna sane da halin matsin tattalin arziki da jama’a ke fama da shi. Wannan lamari yazama kadangaren bakin tulu, ga kuma cutar wanda cutar mashakon numfashi da ta haddasa koma baya da ake fama dashi fiye da shekara guda yanzu”, Ya jaddada.

Daga karshe yayi kira ga mutanen Bauchi da su jure wa wannan hali da addu’oi samun mafita daga matsalolin da suka addabe mu da sauran sassan kasan Najeriya.

Labarai Makamanta