Sakon Sabuwar Shekarar 2023: Duk Wanda ‘Yan Najeriya Suka Zaba Shi Zan Ba Mulki – Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya sake jaddada cewa zai tabbatar wa ‘yan Najeriya da duniya cewa zai tsaya ya tabbatar ya ga an gudanar da zaɓen 2023 lami lafiya, kuma sahihi, karɓaɓɓe babu maguɗi.

A cikin bayanin sa na ƙarshen shekarar 2022, Buhari ya ce duk wanda ‘yan Najeriya su ka zaɓa, shi za a bayyana a matsayin shugaban ƙasa, kuma shi zai damƙa wa mulki.

Buhari ya nuna jimami tare da yin ta’aziyyar waɗanda ya ce “mutuwa ta riske su ba su samu damar ganin ƙarshen shekarar 2022 ba, kuma ba su samu tsallakawa cikin shekarar 2023 ba.

Ya ce a yanzu da shekara ta zo ƙarshe, lokaci ne wanda za a tsaya a yi tambihin baya, a yi nazarin yadda yau ta ke, tare da kirdadon abin da gobe za ta zo mana da shi.

“Wannan shekara ta 2022 ta na da matuƙar muhimmanci a wuri na. Saboda daga yau bai fi saura wata biyar ba na miƙa mulki ga wanda za ku zaɓa.

“Ina tabbatar ma ku da cewa INEC ta tashi haiƙan wajen ganin ta yi zaɓe ingantacce kuma sahihin da zai zama karɓaɓɓe.”

Da ya koma kan wasu muhimman nasarorin da aka samu, Buhari ya ce ‘yan Boko Haram sama da 82,000 da iyalan su ne su ka tuba daga aikata ta’addanci.

Daga nan ya ci gaba da bayyana nasarorin da gwamnatin sa ta samar a cikin 2023 da ma sauran shekaru fiye da bakwai da ya yi kan mulki, waɗanda a yanzu ya ce nan da watanni biyar zai kammala wa’adin sa na shekaru takwas.

Shugaba Muhammadu Buhari ya sake jaddada cewa zai tabbatar wa ‘yan Najeriya da duniya cewa zai tsaya ya tabbatar ya ga an gudanar da zaɓen 2023 lami lafiya, kuma sahihi, karɓaɓɓe babu maguɗi.

A cikin bayanin sa na ƙarshen shekarar 2022, Buhari ya ce duk wanda ‘yan Najeriya su ka zaɓa, shi za a bayyana a matsayin shugaban ƙasa, kuma shi zai damƙa wa mulki.

Labarai Makamanta