Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ce masu son tayar da fitina a ƙasar “sun gaza yin hakan”, yana mai cewa “alkairi na tafe a 2023 da gabanta” cikin jawabin ranar Kirsimetinsa na ƙarshe a matsayin shugaban ƙasa.
Cikin jawabin da ya gabatar a ranar Asabar, Buhari ya jaddada cewa nan da watan Mayu gwamnatinsa za ta miƙa mulki ga sabuwar gwamnatin da za a zaɓa a babban zaɓe na watan Fabarairu.
“Saƙona kenan na Ranar Kirsimeti a matsayin shugaban ƙasa,” in ji shi. “Nan da mako 22 daga yanzu wannan gwamnatin za ta miƙa mulki ga wata.”
Kazalika, ya bayyana miƙa mulkin a matsayin “dama ta tabbatar da kafuwar dimokuraɗiyya a Najeriya kamar yadda ƙasashen waje suka sani”.
A cewarsa: “Mu ci gaba da zama lafiya cikin annashuwa har zuwa sabuwar shekara da kuma lokacin zaɓe a watan Fabarairu da ma gaba.
“Ina tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa waɗanda ke neman tayar da fitina a ƙasarmu sun gaza a yunƙurinsu.”
A wani labarin na daban shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce ‘yayansa biyu ne suka rasu sakamakon cutar Sikila.
Buhari ya bayyana hakan ne ranar Juma’a a wajen wani gagarumin taro da ‘yan uwa da abokan arziki suka shirya masa kan bikin cikarsa shekara 80 da haihuwa a fadarsa.
Yayin da yake jawabi game da rayuwarsa shugaba Buhari ya ce ‘ya’yansa biyu ne – da ya haifa tare da matarsa ta farko mai suna Safinatu – suka rasu sakamakon cutar Sikila.
Ya ƙara da cewa hakan ya tilasta masa yin gwajin ƙwayoyin halitta a lokacin da ya tashi auren matarsa ta yanzu Aisha Buhari.
Ya ce ya dage cewa dole sai matar da zai aura ta kasance tana da ƙwayoyin halitta na AA, don kauce wa ɗaukar cutar Sikila ga ‘yayan da zai haifa kasancewar shi yana da ƙwayoyin halitta na AS.
Buhari ya auri Safinatu a shekarar 1971. sun kuma haifi ‘ya’ya biyar tare da ita.
You must log in to post a comment.