Sakin Nnamdi Kanu Na Bukatar Dogon Nazari – Shugaban Kasa

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce zai yi nazarin buƙatar da ya kira “mai girman gaske” ta neman ya saki Nnamdi Kanu wadda ƙungiyar dattawan al’ummar Ibo suka gabatar masa.

Kanu wanda ake zargi da aikata ta’addanci a gaban kotu, na hannun ‘yan sandan farin kaya na DSS sakamakon gwagwarmayar da yake yi ta neman kafa ƙasar Biafra a kudancin Najeriya ƙarƙashin ƙungiyar Indigenous People of Biafra (IPOB) da aka haramta.

Buhari ya bayyana hakan ne yayin da yake karɓar baƙuncin dattawan a fadarsa da ke Abuja ranar Juma’a ƙarƙashin jagorancin tsohon Ministan Sufurin Jirgin Sama Mbazulike Amaechi.

“Kun nemi abu mai matuƙar girma a wajena a matsayina na shugaban wannan ƙasa. Tasirin buƙatar taku na da girma sosai,” a cewar Buhari cikin wata sanarwa da Femi Adesina ya fitar.

Ya ƙara da cewa buƙatar da dattijan suka nema “ta saɓa wa tanadin tsarin mulki da ya fayyace tsarin shugabanci tsakanin gwamnati da ɓangaren shari’a”.

“Sai dai buƙatar da kuka gabatar mai girma ce sosai amma zan yi nazari a kanta,” in ji shi.

Labarai Makamanta