Sai ‘Yan Mata Sun Bada Kansu Kafin Ake Saka Su A Fim – Sarkin Waka

Shahararren mawakin zamani Naziru Sarkin Waka ya yiwa jagororin Hausa film wankin babban bargo, inda ya bayyana halayyar tsarin ‘yan jari hujja da danniya da lalata da akeyi a Masana’antar

Naziru yace Wallahi ‘yan Hausa film ba Allah a ranku, ya fadi hakane sakamakon hiran da BBC tayi da wata tsohuwar jaruma a Masana’antar Hausa film Ladi Cima inda tace bata samun abinda ya wuce Naira dubu 10, shine sai daraktocin film suka mata caa suna raddi a gareta

Sarkin Waka yace kamar Ali Nuhu da Falalu Dorayi karya suke ace basu san ana yiwa tsofin ‘yan Hausa film wannan wulakanci ba, su tashi aiki a dauki Naira dubu daya ko Naira dubu biyu a biyasu, wani lokacin ma ba babu ko kobo ace za’a kirasu, kuji tsoron Allah mana, kun san anayi

Sarkin Waka yace shi ya san fina-finan da kafin a saka wani a cikin shirin sai ya biya kudi daga aljihunsa ba ma batun wai a biyashi ba, ko kuma ya biya da wani abu makamancin kudi, Sarkin waka yace ko ki bada kudi a sakaki film ko ki bada kanki ayi lalata dake, na rantse da Allah wannan ne abinda yake faruwa, idan su Ali Nuhu da Falalu Dorayi sun isa su fito suyi rantsuwa cewa haka baya faruwa

Labarai Makamanta