Sai Da Muka Ba Da Kiret-Kiret Na Giya Kafin ‘Yan Bindiga Suka Saki Dan’uwanmu – Dangi

Labarin dake shigo mana daga jihar Kano na bayyana cewar ‘yan uwan wani bawan Allah da aka yi garkuwa da shi sun bayyana yadda suka yi yarjejeniya ta kai kiret-kiret na giya ga ‘yan bindiga da naira 500,000 kafin suka saki ɗan uwan mu.


Mukhtar Ibrahim ya gamu da tsautsayin faɗawa hannu ƴan bindiga tun a watan Nuwamba a titin Kaduna-Abuja.

Tun a wancan lokacin kusan wata biyu da wasu kwanaki ya ke tsare a hannun ƴan bindigan ana ta tattauna kuɗin fansa.

An ruwaito cewa tun da farko dai maharan sun bukaci a biya naira miliyan 50 kudin fansa amma kuma hakan bai yiwu ba.

Iyalai da ƴan uwan Mukhtar suka ci gaba da roko da tattaunawa da ƴan bindigan tun a wancan lokacin har suka amince da naira 500,000.

” Haka dai muka yi ta rokon su su rage har suka amince mu biya naira 500,000. Ba kudin ba kawai sun ce mu hado da kiret din giya 6, da na Power Horse 1 sannan kuma da babura guda biyu.

” Yaya za mu yi haka dai da kyar muka iya siyo kiret shida na giya da kuma sauran abinda suka bukata.

Ɗan uwan mukhtar wanda baya so a faɗi sunan sa saboda tsaro ya kara da cewa ƴan bindiga sun gargaɗe su kada su kuskura su saka wani abu da za a fallasa inda suke, ko kuma su saka guba a cikin giyan da za su kawo musu.

” Ko bayan da muka kai musu cikin kungarman daji ba su saki Mukhtar ba sai da suka tabbatar giyar babu matsala.

Labarai Makamanta