Sace-Sacen Ɗalibai: Buhari Na Cikin Tsananin Damuwa – Shehu

Fadar Shugaban kasa ta tabbatar da cewa tana matukar jin kunyar yadda ake yawan sace daliban makaranta a kasar nan musanman yankin Arewacin kasar mai yawan jama’a.

Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa a harkar yada labarai, Garba Shehu, ya sanar da hakan a ranar Juma’a.

Yace yadda ake yawan sace ‘yan makaranta yana matukar ba shugaban kasa Muhammadu Buhari kunya a gida Najeriya da ketare.

Ya sanar da hakan ne a wata tattaunawa da yayi a shirin gari ya waye na gidan talabijin din Channels.

Shehu yayi jawabi a kan koma bayan da aka samu a bangaren garkuwa da ‘yan makaranta ballantana a yankin arewa Ya tabbatar da cewa shugaban kasa ya san komai dake faruwa a kasar nan inda ya kara da cewa “mafi gaggawan hanyar isar da sako ga shugaban kasa shine ta manema labarai da kuma fallasa duk wani mugun abu dake faruwa kasar nan.”

Garba Shehu yace Buhari na da ra’ayin hada kan ‘yan Najeriya tare da kawo karshen matsalolin tsaron da suka addabi kasar nan. Ya kara da jaddada cewa ‘yan Najeriya suna morar ‘yancin fadin ra’ayinsu karkashin mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

A bangaren ta’addanci, ya jajanta yadda wasu masu yada labarai ke bayyana labaran miyagu tamkar wasu masu aiki nagari.

Labarai Makamanta