Sace Ma’aikatan Kananan Hukumomi: Dalibai Sun Yi Barazanar Kulle Birnin Zazzau

Ƙungiyar Ɗalibai ta Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Ƴan Arewa, tayi barazanar kulle Birnin Zaria a Jihar Kaduna, sakamakon sace Ma’aikatan Ƙananan Hukumomi 13.

Majiyar Jaridar Dimokuraɗiyya tace an sace su ne a lokacin da suka dawo daga ziyarar ta’aziyya.

An dai bada rahoton cewa an sace su ne a Kidandan ta Ƙaramar Hukumar Giwa dake Jahar Kaduna a ranar Litinin.CNG

Wata majiya ta tsaro ta nuna cewa Umar Abubakar (Katako) direban mota mai kujeru 18, daya ɗauko su, sun sako shi.

Sun umarce shi daya tafi, tare da sanar da ƴan uwan wanda lamarin ya shafa cewa sun sace Ma’aikatan.

Yace a rahoton gani da ido, ƴan bindiga guda 6, da bindiga ƙirar AK-47 sun tsayar da motar tare da sace mutanen ciki, mintuna 45 bayan ta bar ƙauyen Kaya.

Ya ƙara dacewa, bayan sunyi bincike tare da tafiya da kayayyakin matafiyan, sun tafi dasu cikin daji

Labarai Makamanta