Sace Ɗaliban Kagara: Buhari Na Fuskantar Matsin Lamba Daga Waje

Ƙungiyoyin ƙasashen duniya na ci gaba da matsa wa hukumomin Najeriya lamba, don ceto ɗaliban nan su kusan 50, da masu satar mutane suka yi awon gaba da su daga wata makarantar Sakandire ta Kagara a jihar Neja.


Da sanyin safiyar ranar Talata ne wasu ƴan bindiga suka sace ɗaliban da kuma wani malaminsu da iyalinsa shida mata da ‘ya’ya, a makarantar sakandiren garin Kagara da ke jihar Neja a arewacin Najeriya.

A wannan karon hukumar kula da ƙananan yara ta Majalisar Ɗinkin Duniya wato UNICEF ta ce tana cike da matuƙar tashin hankali a kan sace gomman ɗaliban, da kuma yadda aka kwashe fiye da kwanaki uku ba tare da an ji wani batu mai gamsarwa dangane da shirin da ake yi na ceto su ba.


Cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta ce abin takaici ne yadda ake samun hare-hare a makarantun ƙananan yara, duk da cewa ƴancinsu ne su nemi ilimi ba tare da wani sharaɗi ba.

Yadda ƴan bindiga ‘suka kashe abokina suka tafi da ƴan uwana ɗalibai a GSS Kagara’
Sace-sacen ɗalibai a makarantu huɗu da suka girgiza Najeriya
Illar bai wa masu satar mutane kudin fansa a Najeriya.


Ta kuma yi kira ga hukumomin Najeriya su tashi tsaye wajen tabbatar da kare makarantu musamman na kwana, ta yadda tsarin ilimi a Najeriya zai ci gaba da wanzuwa ba tare da wata barazana ba.


Amurka da wasu manyan ƙasashen duniya, da kuma Majalisar Dinkin Duniya sun yi Allah wadai da sace ɗaliban, tare da yin kiran sakinsu ba tare da ɓata wani lokaci ba.

Shi dai shugaba Muhammadu Buhari ya bada umurnin ceto ɗaliban a cikin aminci, tuni kuma ya tura tawagar wasu jami’an gwamnatinsa zuwa zuwa jihar ta Neja domin jagorantar kuɓutar da su.

Wasu rahotanni da aka samu a ranar Alhamis, sun bayyana cewa gwamnatin jihar ta fara tattaunawa da maharan da suka sace waɗannan ɗalibai.

Wasu majiyoyi sun shaidawa jaridar Daily Trust cewa wasu tubabbun yan bindiga da kuma wasu jagororin Fulani ne ke jagorantar tattaunawar domin ganin an kuɓutar da ɗliban lami lafiya.

Wasu masana kan lamuran tsaro dai ga ganin cewa da alama mahukuntan Najeriya basu ɗauki wani darasi daga abubuwan da suka faru a baya, na sace ɗalibai a wasu makarantu da ke arewacin ƙasar ba.

Labarai Makamanta