Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

Sabuwar Najeriya: Ba Zan Yi Gwamnatin Hadin Kai Ba – Tinubu

Zababben shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya yi watsi da rahotannin da ke cewa zai kafa gwamnatin hadin kai domin janyo kowanne bangaren siyasar kasar wajen yin aiki tare. 

Wata sanarwar da ya raba wa manema labarai mai dauke da sanya hannunsa ta bayyana Tinubu na cewa bukatarsa ta zarce haka, a matsayinsa na wanda zai yiwa jama’a hidima, yayin da ya bayyana cewar shi da abokan tafiyarsa suna can suna ta tattaunawa da gudanar da tarurruka domin ganin gwamnatinsa ta fara da kafar dama da zarar ta fara aiki. 

Tinubu yace a matsayinsa na shugaban jama’a wanda ya amince da nauyin da aka dora masa, ana ta batun kafa gwamnatin hadin kai, amma shi abinda yake tunani ya zarce haka. 

Zababben shugaban yace yayin nada wadanda za suyi aiki da shi ba zai yi watsi da kwarewa ba da kuma irin rawar da jama’a suka taka a baya, domin lokacin siyasa ya wuce. 

Tinubu yace zai tattara jajartattun mutane maza da mata a fadin Najeriya domin gina kasa mai inganci da kuma adalci ga kowanne ‘dan kasa, yayin da matasa zasu samu damar taka rawar da ta dace da su, ciki harda mata. 

Shugaban yace babu wanda zai shiga gwamnatinsa saboda zuwa Mujami’a ko Masallachi domin yin ibada, sai dai saboda hali da kuma kwarewa, yayin da ya kara da cewa saboda haka ba za suyi watsi da haka ba wajen nada wadanda basu cancanta ba. 

Tinubu ya bukaci wadanda suka zabe shi da su ci gaba da amincewa da manufofinsa da kuma shirin da yake da shi ga Najeriya, yayin da ya shaidawa wadanda basu zabe shi ba da su ci gaba da imani da Najeriya ba tare da la’akari da banbancin siyasa ba. 

‘Yan Najeriya sun dade suna rade radin cewar zababben shugaban zai rarraba mukamai ga bangarori daban daban ciki harda wadanda basu zabe shi ba, amma kuma ga alama wannan sanarwa ta kawo karshen wannan hasashe. 

Exit mobile version