Sabuwar Cuta Ta Ɓulla A Jihar Bauchi

An tabbatar da ɓullar wata sabuwar cuta wacce ke sanya kumburin ƙafafuwa a ƙauyen Burah ƙaramar hukumar Kirfi da ke jihar Bauchi, kuma ya zuwa yanzu mutane 10 sun kamu da wannan cuta.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga babban shugaban hukumar kiwon lafiya daga matakin farko ta jihar (BASPHCDA), Dr Rilwanu Mohammed, ya yin tattaunawa da manema labarai a ranar bukin cututtukan da aka yi watsi da su na duniyaa shekarar 2021, da ya gudana a ranar Litinin.

Rilwanu Mohammed ya ce: “A yammacin ranar Lahadi, mun samu rahotanni kan cewar akwai cutar da ta ɓulla mai kumbura ƙafafuwa, kuma ya zuwa yanzu mutane 10 sun kamu.

“Na umurci sashen dakile yaduwar cututtuka da ke a hukumar da ya ziyarci ƙauyen domin yin bincike kan wannan sabuwar cuta.”

“Muna hasashen cewa kwayar cutar “onchocerciasis” ko kuma “lymphatic filariasis” ce ta kama mutanen la’akari da cewa karamar hukumar na fama da cututtukan daji.

Da zaran mun samu tabbacin cutar da ke damun su, za mu dauki matakin da ya dace don dakile yaduwar cutar.”

Dangane da bukin ranar NTDs, shugaban hukumar BASPHCDA ya ce mafi akasarin cututtukan da suka shafi muhalli da daji suna zuwa ne sakamakon rashin tsabtataccen ruwan sha, inda sama da mutane miliyan 1 ne suke fama da ire Iren wadannan cutukan.

Cututtukan muhallin da aka fi yin biris da su, sun hada da: Onchocerciasis, lymphatic filariasis, soil-transmitted helminths, trachoma, schistosomiasis, Buruli ulcer, snake bite, leprosy, human African trypanosomiasis, Guinea worm, yaws da kuma loiasis.

Sannan ya ce za a iya magance wadannan cututtukan ne ta hanyar tsaftar muhalli da ta jiki.

Ya yi nuni da cewa ya zuwa yanzu, jihar Bauchi na fama da cutar “Onchocerciasis” a kananan hukumomi 12; “lymphatic filariasis” a kananan hukumomi 11; “Schistosomiasis” a kananan hukumomi 16; “Trachoma” a kananan hukumomi 2 sai kuma “Guinea worm” wacce tuni aka kawo karshen ta a fadin Nigeria.

Rilwanu Mohammed ya kara da cewa sashen kula da kuma dakilewa na kuma gwamnatin jihar na aiki kafada da kafada da asusun UNICEF da kuma wata kungiya mai rajin taimakawa marasa galihu (MITOSATH) domin shawo kan matsalar.

Labarai Makamanta

Leave a Reply