Sabunta Rijista: An Yi Kira Ga Shugabannin APC

An yi kira da babbar murya ga shugabannin Jam’iyyar APC mai mulki da sauran masu ruwa da tsaki a jam’iyyar da cewa, suyi dukkanin mai yiwuwa wajen ganin sun shawo kan matsala ta korafi da ‘ya’yan jam’iyyar ke yi na zargin ɓoye katuttukan zama ɗan jam’iyya da ake zargin wasu da yi.

Kiran ya fito ne daga bakin wani jigo a jam’iyyar ta APC a Jihar Kaduna Alhaji Abdullahi Gambo Abba Jakadan Hayin Banki, jim kaɗan bayan kammala sabunta rijistar zama ɗan jam’iyya da yayi a mazaɓar shi dake Hayin Banki Kaduna.

Gambo Abba ya cigaba da cewar ko shakka babu jam’iyyar APC tana nan da farin jinin jama’a kamar yadda aka santa tun asali, ta la’akari da yadda jama’a ke tururuwa wajen sabunta rijistar zama ɗan jam’iyya, sai dai babbar matsalar da ake fuskanta ita ce ƙarancin katuttukan jam’iyyar, wanda hakan ke haifar da damuwa kuma ba ƙaramar barazana bace ga jam’iyyar.

Jakadan Hayin Banki ya buƙaci Shugabannin jam’iyyar da sauran masu ruwa da tsaki su binciki zargin ɓoye katuttukan da ake yi, domin akwai zargin cewa ana ɓoye katuttukan ne domin wata manufa da ake son amfani da ita a lokacin zaɓukan fidda gwani, inda wasu ke burin sai nasu ne kawai za su kai labari.

Gambo Abba wanda ya taɓa tsayawa takarar Kujerar ɗan Majalisar dokokin Jihar Kaduna mai wakiltar mazaɓar Kawo a jam’iyyar APC a zaɓen da ya gabata, ya sha alwashin cigaba da bayar da dukkanin gudummuwar shi wajen ganin APC ta cigaba da samun tagomashi a matakin ƙaramar Hukumar Kaduna ta Arewa dama jiha baki ɗaya.

Labarai Makamanta