Sabon Shugaban EFCC Ya Tsallake Siraɗin Majalisa

Majalisar dattawan Najeriya ta amince da AbdulRasheed Bawa a matsayin sabon shugaban hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa watau EFCC.

Shugaban majalisa, Sanata Ahmad Lawan, ya sanar da hakan a zauren majalisan ranar Laraba, 24 ga Febrairu, 2021.Wannan ya biyo bayan tambayoyi da ya amsa yayinda ya gurfana gaban yan majalisan.

Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, Sanata Babajide Omoworare ne ya gabatar da Bawa wanda tuni ya kasance a dakin taron.

A bayanan Bawa yayi alkawarin baiwa matasan najeriya kyakkyawar wakilci a hukumar EFCC, Sannan yayi alkawarin kawo sauyi tare da yin aiki kan gaskiya a hukumar ta EFCC

Labarai Makamanta