Sabon Shugaban Dakarun Soji Ya Shiga Ofis

Rahotanni daga babban birnin tarayya Abuja na bayyana cewar sabon Shugaban Dakarun Soji Manjo Janar Farouq Yahaya a ranar Juma’a 28 ga Mayu, ya fara aiki a matsayin Shugaban Sojojin Najeriya na 22 a Hedikwatar Soji da ke Abuja.

Ya fara aikinsa ne cikin zimma ta hanyar duba masu tsaron Kwatas da duba sauran muhimman bayanan tsaron ƙasa.

A ranar Alhamis 27 ga watan Mayu ne hedikwatar tsaron ta sanar da nadin da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi wa Yahaya a matsayin sabon Shugaban Dakarun Sojin.

Sabon Shugaban Dakarun Sojin ya kai ziyarar karramawar karshe ga tsohon shugabansa kuma wanda ya gada, Lt-Gen Ibrahim Attahiru. Manjo-Janar Yahaya ya yi mubaya’a ga marigayi Attahiru ne bayan sanya hannu a rajistar ta’aziyar a hedkwatar rundunar Operation Hadin Kai da ke yankin Maimalari, Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Janar Attahiru da wasu hafsoshin soja 10 sun mutu a wani hatsarin jirgin sama a Kaduna a ranar Juma’a, 21 ga Mayu.

Labarai Makamanta