Sabon Kamfanin Jirgin Saman Najeriya Zai Fara Aiki A Shekarar Badi – Sirika

Ministan Sufurin jirgin sama, Sanata Hadi Sirika, ya bayyana cewa sabon kamfanin jirgin sama mallakin gwamnatin tarayya, Nigeria Air zai fara aiki a farkon shekarar 2022 dake tafe.

Sirika ya bayyana hakan ne yayin hira da manema labarai a fadar shugaban kasa bayan taron majalisar zartaswar a Abuja a ranar jiya Laraba.

Sirika ya ce an dade da shirin samar da wannan kamfani na kasa kuma zai fara aiki a farkon 2022, da farashi mai sauki fiye da kamfanoni masu zaman kansu.

Sirika ya ce wannan sabon kamfanin jirgin zai taimakawa yan Najeriya wajen samar da aikin yi ga miliyoyin mutane. Ya ce annobar COVID-19 ce ta sabbaba dage shirin kaddamar da kamfanin zuwa karshen 2021.

Labarai Makamanta