Sabani Da Saurayi: Dalibar Jami’ar Katsina Ta Kwankwadi Guba

Rahotannin dake shigo mana daga jami’ar Umaru Musa Yar’adua dake jihar Katsina na bayyana cewa wata daliba ta sha guba saboda wani sabani tsakaninta da saurayinta.

Majiyarmu ta tattaro bayanan cewa ana kyautata zaton cewa dalibar ‘yar aji uku ce a sashen nazarin zamantakewa na ‘Sociology’ a jami’ar.

Majiyar ta dogara da ita daga cikin jami’ar da ta nemi a sakaya sunanta, ta ce ana zargin saurayin dalibar da shi ma tsohon dalibi ne a jami’ar da ya kammala karatu a shekarar bara ne ya yanke hukuncin cewa zai rabu da budurwar ta sa, dalilin da ya sa ta dauki wannan mataki.

Sai dai, duk ba a ambaci sunan dalibar ba, bayanai sun tabbatar da cewa tun daren Juma’a wayewar Asabar, dalibar na asibitin jami’ar, amma dai wasu bayanai sun ce an mayar da ita wani asibiti a cikin Katsina.

Bayanai da suka fito daban-daban, sun ce dalibar ta sha maganin kashe kwari na ‘insecticides’, wasu su ce ta sha ‘septol’ wasu ma na cewa ‘sanitizer’ ta sha, wasu na cewa ‘fiya-fiya’.

Duk da dai babu bayanin cikakken halin da dalibar ke ciki, amma dai bayanai sun tabbatar da cewa har yanzu tana asibiti, likitoci na duba lafiyarta.

Labarai Makamanta