Ruwa Ba Sa’an Kwando Bane: Na Yi Wa Abokanan Takarata Fintinkau A Ilimi – Kwankwaso

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar ɗan takarar shugabancin kasa a ƙarƙashin Jam’iyyar NNPP mai kayan marmari Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso a ziyarar da ya kai Jihar Katsina ya bayyana fifikon dake tsakanin shi da sauran ‘yan takarar shugabancin kasa musamman Tinubu da Atiku.

A bangaren ilmin zamani, Kwankwaso ya ce yayin da shi yake da PhD a bangaren ilmin ruwa, sauran ‘yan takaran ba su wuce ilmin sakandare da difloma ba. Tsohon Gwamnan ya ce ya yi shekaru 17 yana aikin ruwa a Kano, sannan ya yi shekaru 30 ana gwabzawa da shi a siyasa, ya rike mukamai dabam-dabam.

Dan takaran Shugabancin Najeriya a NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso zai yi jawabi a gaban Duniya a dakin taro na Chatham House. A tsakiyar watan Junairun 2023.

Labarai Makamanta