Rushe Shugabannin APC A Kano Ya Shafi Mazaɓu Kawai Ne – Kwamishina

Rahotanni daga Jihar Kano na bayyana cewar Jam’iyyar APC)a jihar ta ce hukuncin da wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yanke a ranar Talatar da ta gabata ya shafi zabukan mazabu ne kawai, banda shugabannin jam’iyyar na jiha dana kananan hukumomi.

A wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar, Malam Muhammad Garba ya fitar, ya ce tsarin jam’iyyar a jihar hedikwatar jam’iyyar ta kasa ta amince da shi.

Sai dai ya ce jam’iyyar ta shigar da kara ne domin daukaka karar hukuncin da babbar kotun tarayya ta yanke da kuma daukar mataki kan lamarin.

Malam Garba ya yi kira ga ‘yan jam’iyyar da su kwantar da hankulansu su ci gaba da gudanar da ayyukansu kamar yadda kundin tsarin mulkin jam’iyyar ya tanada.

Labarai Makamanta