Rungumar Zaman Lafiya Ne Mafita Ga ‘Yan Najeriya – Tsohon Shugaban Kasa

Tsohon Shugaban kasa kuma shugaban kwamitin zaman lafiya na kasa, Janar Abdulsalami Abubakar mai ritaya ya nemi a rungumi zaman lafiya kan abubuwan da suka faru kwanan nan na hare-haren kabilanci a fadin kasar.

Hakazalika ya bukaci sabbin shugabannin tsaro da Sufeto-Janar na ‘yan sanda a kan su tashi tsaye a wannan lokacin don shirya kyawawan dabarun kawo karshen mummunan abubuwan da ke faruwa a kasar.

Abdulsalami wanda ya nuna rashin jin dadinsa game da rikice-rikicen da ke faruwa a kasar, ya koka kan cewa idan ba a kula da abubuwan da ke haifar da rabuwar kai, rashin tsari da wargajewar da ke yaduwa cikin sauri a fadin kasar za su kai ta ga matakin da ba a dawowa.

Da yake zantawa da manema labarai a gidansa na Uphill da ke Minna, shugaban kwamitin zaman lafiyar na kasa ya yi kira da a kwantar da hankula. Ya kuma bukaci kowa ya hada karfi da karfe a kokarin shawo kan matsalolin da ke faruwa wanda zai taimaka matuka wajen ganin kasar ta ci gaba da kasancewa tsintsiya daya.

“Gaskiya ne cewa dukkanmu muna cikin wani yanayi na tsoro da tarin damuwa. Sai dai kuma, abu na ƙarshe da muke buƙata shi ne abokan gaba su samu rashin hadin kai a ɓangarenmu.

“Mu, a kwamitin zaman lafiya na kasa muna so mu kara muryoyinmu ga muryoyin miliyoyin‘ yan Najeriya da ke kira da a kwantar da hankali a wannan mawuyacin lokaci.

“Wadannan lokutan na bukatar dukkanmu mu hada hannu waje guda don warware matsalolin da za su hada kan kasarmu. Babu abun tsinta wajen daura wa juna laifi,” in ji shi.

Abdulsalami ya kara da yin kira ga mutanen da ke jin ciwon abunda ke wakana a kasar da su kasance masu juriya da hakuri inda ya kara da cewa akwai bukatar kowa ya taru wuri daya, ya sadaukar da kai da kuma kasancewa a ankare.

Tsohon Shugaban kasan ya gargadi gwamnonin jihohi da su janye takobin su, su daina maganganun su tare da daukar cikakkiyar alhakin kula da lamura a cikin jihohin su.

Daga nan sai ya bukaci majalissun gargajiya, shugabannin addinai da kungiyoyi masu zaman kansu da su tara ’yan Najeriya tare da wayar musu da kai kan bukatar zama lafiya da junansu.

Abdulsalami ya yaba wa Shugaba Buhari kan daukar dukkan matakai wajen tabbatar da cewa an rage tashin hankali a faɗin ƙasar.

Labarai Makamanta