Rungumar Akidar Zaman Tare Shine Mafita Ga Matsalolin Najeriya – Sarkin Musulmi

Mai alfarma Sarkin Musulmi kuma shugaban Majalisar Koli ta Addinin Musulunci Dakta Muhammad Sa’ad Abubakar ya bukaci al’ummar Musulmi da sauran jama’ar Najeriya da rungumar akidar zaman tare da juna domin samun dawwamamen zaman lafiya kasar.

Sarkin Musulmin ya bayyana haka ne a wurin taron bikin cikarsa shekaru 15 kan karaga a matsayin Sarkin Musulmi na 20 a Daular Usmaniyya.

Dr Sa’ad Abubakar ya bada tabbacin haɗin guiwa da al’umma domin bada gudunmawarsu wajen magance dimbin matsalolin da ke addabar Najeriya musamman yankin arewacin kasar.

Babban Malamin addinin Islama Sheikh Ismael Mufti Menk na Zimbabwe, shi ne bakon da ya gabatar da makala mai taken “ Koyarwar addini da zamantakewa domin samun zaman lafiya a kasashe masu tasowa”

A yayin gabatar da makalar, Menk ya bukaci Musulmai da su guji kyamatar jama’a tare da mutunta sauran addinai.

Tuni shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aike wa Sarkin Musulmin da sakon taya shi murnar cika shekaru 15 kan karagar mulki.

Labarai Makamanta