Rundunar ‘Yan Sanda Ta Musanta Afkuwar Hatsari Ga Jirginta

Rundunar ƴan sandan Najeriya ta musanta rahotannin da wasu kafofin yaɗa labaran Najeriya ke cewa wani jirgi mai saukar ungulu mallakarta ya yi hatsari a Bauchi.

Rundunar ta kuma musanta labaran da ke cewa waɗanda suke cikin jirgin sun samu munanan raunuka.

Rundunar ta ce jirgin wanda ya taso daga Abuja a ranar 26 ga watan Janairun 2022 ya yi saukar gaggawa ne a filin jirgin sama na Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi.

Rundunar ta ce duka mutane shida da ke cikin jirgin lafiyarsu kalau haka kuma rundunar ta ce direban jirgin ƙwararre ne wanda a dalilin haka ne ya sa ya sauka lafiya ba tare da jirgin ya yi dameji sosai ba.

Rundunar ta ce farfelar jirgin ta baya ce kawai ta samu matsala a yayin sauka.

Labarai Makamanta