Rundunar ‘Yan Sanda Ta Dakatar Da Dan Sandan Da Ya Harbe Lauya A Legas

Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Sufeto janar na rundunar ‘yan sanda, Usman Alkali Baba ya ba da umarnin a dakatar da wani jami’in dan sanda, Drambi Vandi biyo bayan bindige wata mata lauya, Bolanle Raheem.

Bolanle, wacce lauya ce kuma matar aure ta gamu da ajalinta a hannun Drambi, lokacin da ta yi arba dashi a jihar Legas a ranar Kirsimeti da ta gabata a cikin motar ta.

Rahotanni sun bayyana cewar Lauyar tana dauke da juna biyun tagwaye a lokacin da wannan dan sanda ya dirka mata bindiga ya kashe ta.

Umarnin IGP na zuwa ne ranar Laraba 28 ga watan Disamba daga cikin wata sanarwa da Myiwa Adejobi; kakakin rundunar ‘yan sandan Najeriya ya fitar.

A cewar sanarwar, dakatar da jami’in ya yi daidai da matakin ladabtarwa da hukumar ke dauka kan jami’an da ke saba doka da kuma daukar doka a hannu.

Labarai Makamanta