Rundunar ‘Yan Sanda Ta Bada Umarnin Tsaurara Tsaro A Ofisoshin INEC

Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya IGP Usman Alkali Baba ya umarci kwamashinonin rundunar na jihohi da su ƙaddamar da tsarin ba da kariya ga ayyukan babban zaɓe na 2023 da ke ƙaratowa.

Kazalika, babban sufeton ya umarce su da su tabbatar da tura dakarun kwantar da tarzoma zuwa wuraren da suka dace.

“Sufeto janar ya bayyana cewa tashin hankali da kalaman ƙiyayya da barazana da rashin jimuri da yaɗa labaran ƙarya da tsattsauran ra’ayin siyasa baraza ne ga dimokuraɗiyyarmu da tsaron ƙasa,” a cewar sanarwar da Kakakin ‘Yan Sanda na Ƙasa Olumuyiwa Adejobi ya fitar a yau Lahadi.

Tsarin ya ƙunshi yin aiki tare da sauran jami’an tsaro na ƙasar da kuma tattaunawa da masu ruwa da tsaki don lalubo hanyoyin tsaurara tsaro a ofisoshin hukumar zaɓe ta INEC.

Labarai Makamanta