Rundunar Sojin Najeriya Ta Yi Wa Manyan Hafsoshi Ritaya

Labarin dake shigo mana daga Hedkwatar tsaro ta ƙasa na bayyana cewar Rundunar Sojojin Najeriya ta yi wa wasu Janar-janar har 12 ritaya.

An yi wa waɗanda aka yi wa ritayar faretin bankwana a Cibiyar Horas da Zaratan Sojoji ta Jaji, ranar Juma’a, a Kaduna.

Waɗanda aka yi wa ritayar sun haɗa da Manjo Janar shida, Burgediya Janar biyu da kuma wasu manyan hafsoshi biyu.

Manjo Janar ɗin da aka yi wa ritaya ɗin sun haɗa da Lamidi Adeosun, I. Birigini, C.M Abraham, E.C.C Agundu, T.O.B Ademola, A.M Jalingo da A.S Maikobi.

Burgediya Janar biyu da aka yi wa ritaya kuma sun haɗa da M.A Bashrudden da Dam Onayiveta.

Akwai kuma sauran hafsoshi biyu da su ma ritayar ta shafe su.

Da ya ke jawabi a wurin faretin wanda aka shirya a taron laluben makamar inganta tsaron ƙasa na kwanaki huɗu da aka shirya a Jaji, Kaduna, Adeosun ya yi godiya da bankwana a matsayin kan sa da sauran waɗanda aka yi wa ritayar.

Ya gode wa Allah da ya yi masu tsawoncin rai har su ka kawo ranar da ritayar su ta zo daga aikin soja.

Ya yi kira ga na baya su ci gaba daga inda su su da suka tafi suka tsaya.

Sannan kuma ya gode wa Babban Hafsan Sojojin Najeriya, Farouk Yahaya da shi da Kwamandan Jaji, Manjo Janar Victor Ezugwu.

Labarai Makamanta