Rundunar Soji Ta Kama Jami’inta Dake Da Hannu A Harin Kwalejin NDA

Labarin dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar rundunar sojin sama ta kama Torsabo Solomon, wani Sajan da ake zargi da hannu a kai hari a makarantar horas da sojoji ta Najeriya (NDA) da ke Kaduna.

An kashe jami’ai biyu, an kuma yi garkuwa da wani jami’i guda a lokacin da wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne suka kai wa NDA hari a watan Agusta.

Wannan lamarin ya haifar da hargitsi a kasar tare da nuna damuwa game da karuwar rashin tsaro. Majiyar soja ta shaida cewa an kama Solomon ne a ranar Litinin a NAF’s 153 BSG a Yola, babban birnin jihar Adamawa.

An ce umarnin kama shi ya fito ne daga Manjo Janar IM Yusuf kwamandan NDA. Kafin kama shi, Solomon na hidima a Air Force Comprehensive School da ke Yola.

Ana kuma zargin jami’in da sayar da makamai da alburusai ga ‘yan bindiga da masu aikata laifuka. Bayan kama shi, an ce an kai shi NDA da ke Kaduna domin ci gaba da bincike.

Labarai Makamanta