Rundunar Soji Sun Yi Mini Munmunar Fahimta – Dr. Gumi

Sheikh Ahmad Abubakar Gumi ya yi ƙarin haske kan kalaman da ya yi bayan da rundunar sojin Najeriya ta gargaɗe shi kan abin da ta ce kalaman da ka iya tada husuma.

Sai dai Sheikh Gumi ya ce rundunar sojin ba ta fahimce shi ba ne.

Ya ce batun da ya yi na cewa akwai bara-gurbi a rundunar, yana nufin a shekarun 2010 zuwa 2015 ne.

“Da nake magana kan matsalolin da ke rundunar sojin Najeriya, ina nufin lokacin shekarun 2010 zuwa 2015 ne, lokacin da wasu mutane da ke rike da madafun iko a rundunar suka bari mugayen abubuwa su kai ta faruwa.”

“A lokacin ne aka rika sa abubuwan fashewa har muka rasa wani babban Janar ɗin soja. Ni kaina na tsallake rijiya da baya da aka sa min abin fashewa,” ya shaida wa BBC.

Sheikh Gumi ya bayyana wa BBC cewa yana da kyakkyawar fahimta da rundunar sojin Najeriya kuma babu abin da ya sauya

Labarai Makamanta