Rugujewar Gini: An Tabbatar Da Mutuwar Mutum 20 A Legas

Rahotanni daga birnin Ikko na Jihar Legas na bayyana cewar Hukumar bayar da agajin gaggawa ta ƙasa NEMA ta ce adadin mutanen da suka mutu a benen da ya ruguje a Ikoyi Lagos ya ƙaru, inda yanzu suka kai mutum 20.

A ranar Litinin ne dogon benen mai hawa 22 ya rushe a unguwar Ikoyi a Legas cibiyar kasuwanci a Tarayyar Najeriya.

Hukumomin Lagas sun ce an ciro ƙarin gawar mutum 14 da suka mutu kuma ana tunanin adadin zai iya ƙaruwa. An kuma yi nasarar ceto mutum tara a raye daga ginin, waɗanda ake kula da su a asibiti.

Gwamnan Legas Babajide Sanwo-Olu ya dakatar da shugaban hukumar kula da gidaje ta jihar, yayin da ƴan sanda ke ci gaba da bincike domin gano dalilin rushewar ginin.

An samu rugujewar gine-gine da dama a Lagos a ‘yan shekaru nan.

Labarai Makamanta