Rikicin Shi’a: Kwararrun Likitoci Daga Kasar Waje Sun Gana Da Ibrahim El-Zakzaky

A karon farko, gwamnatin tarayya ta amince ma wasu likitocin kasar waje samun ganawa da shugaban ‘yan shia Ibrahim Zakzaky domin duba lafiyar sa tun bayan kama shi a shekara ta 2015.

Likitocin dai sun samu ganawa da El-Zakzaky ne bayan samun umarni daga Alkalin wata babbar kotu da ke Kaduna, wanda ke sauraren karar da gwamnatin jihar ta shigar da Malamin.

Duba da halin rashin lafiya da El-Zakzakky ke ciki ne ya sa Alkalin ya umarci hukumar tsaro ta farin sirri su gaggauta gayyato masa likitocin da ya ke so domin su duba lafiyar sa da na matar sa.

Tunda farko lauyan El-Zakzaky Femi Falana ne ya nemi wannan bukata daga Alkalin kotun, bayan ya ba ta bayanin cewa har yanzu malamin da matar sa su na fama da matsanancin ciwo sakamakon raunuka da su ka samu daga harbin bindiga da Sojoji su ka yi masu a shekara ta 2015.

Hukumar tsaro ta farin kaya DSS dai ta bi umarnin kotun, inda ta ba likitocin damar ganawa da El-Zakzaky da matar sa a ranar Alhamis, 25 ga watan Afrilu, sai dai ba su bayyana wa manema labarai komai game da abin da ke damun Malamin ba.

Related posts