Rikicin Ganduje Da Shekarau Alhakina Ne – Kwankwaso

Tsohon gwamnan Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ɗora alhakin rikicin da jam’iyyar APC a jihar Kano ta faɗa kan abun da ya kira ”Son rai, irin na gwamnan jihar mai ci Abdullahi Umar Ganduje”.

Yayin wata hira da sashen Hausa na BBC, Kwankwaso ya ce ko kaɗan bai yi mamakin rashin jituwar da ta dabaibaye jam’iyyar da ke jagoanci a jihar Kano ba, tuntuni ya san haka za ta faru, batu ne kawai na lokaci.

”Duk wanda yake ba zai iya rike wanda ya masa alheri shekara da shekaru ba, wanda shi ma da kansa yana fada cewa na masa, amma shi randa ya samu dama rana daya tak ya kasa iya rike Kwankwaso da ‘yan Kwankwasiyya, to kaga ai ba zaman lafiya” inji Kwankwaso.

Sanata Kwankwaso, ya ce ba bu abun da ya yi tasiri a rikicin jam’iyyar ta APC a Kano face tsagwaron son rai da son zuciya, da kuma rashin haƙuri. ”Ni abun ya ma sake tabbatar min da abun da nake zato ne kawai” inji shi.

Ya kara da cewa dama Hausawa kan ce ƙarya fure kawai take ba ta ‘ƴa’ƴa, don haka ga shi lokacin da ake jira ya zo.

A hirar ta sa da BBC, tsohon gwamnan na Kano Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce ya ji dadin kalaman da tsohon gwamnan Jihar Malam Ibrahim Shekarau ya yi na yabonsa, yana cewa duk wanda aka yi wa irin wannan yabo dole zai ji dadi.

Kwankwaso ya ce ”Na samu labarin maganar da ya yi a kaina, amma kawai sai na godewa Allah, ka ga da kamar bai gane bane sai yanzu Allah ya nusar da shi, duk mai hankali zai ji dadi, sannan a matsayinsa ma ace ya saki jiki ya yi wannan magana to na san maganar ta kama jikinsa da gaske yake yi”

Ya kara da cewa ”Don siyasa ta sake hadamu sai a tafi, idan ma bata hada ba sai a godewa Allah, tun da an samu ci gaba a tunaninsa ga shi yana fadar yadda al’amarin yake.

Da yake amsa tambayar BBC kan ko ya ga sakon taya murnar cikarsa shekara 65 da gwamnan Kano mai ci Abdullahi Umar Ganduje ya aika masa ?, sai Kwankwaso ya ce bai gani ba domin aiki ya masa yawa.

”Ina ta aikace-aikace ban sani ba, in da haka yake tun da farko da ba haka ba, duk wanda ya sanni ba wanda zai zo ya ce ya fadi wani abu a kan Ganduje na saurare shi, domin dukkaninsu Kwamishinoni sun sani da sauran ma’aikata da mutan gari, domin idan kace mutum yana da laifi daya amma yana da dai-dai guda tara sannan kace za ka kalle shi da wannan laifin ai ka ga akwai matsala”

Ya kara da cewa ”Na zauna da mutane lafiya ciki har da Ganduje, haka muka bar gwamnati muka koma ma’aikatar tsaro, haka muka yi tsari ya tafi Chadi, haka kuma yana can na ce ya sauka ya dawo gida mu yi aiki da shi, ya dawo na dauki fom din mataimakin gwamna na bashi, na ce kai ne babba, ba tare da ko sisin Kwabo ba, domin mu a tsarinmu na Kwankwasiyya ba wanda zai ce ka bada ko sisin Kwabo”

Sai dai a cewar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, duk da wadannan alherai da ya yi wa tsohon mataimakin nasa, sai ga shi a yanzu shi da shi ya fi adawa a kan kowa.

Labarai Makamanta