Rikicin Boko Haram Ya Lakume Rayuka Sama Da 100,000 – Hukumar Tsaro

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar babban hafsan tsaro na ƙasa Janar Lucky Irabor,ya ce rikicin Boko Haram ya yi sanadin mutuwar mutum 100,000, yayin da ya raba mutum miliyan biyu da muhallansu tare kuma da janyo hasarar kusan naira tiriliyan 3.24.

Janar Iroba na fadin haka a ranar Talata a lokacin rufe bikin bitar ayyukan ministocin kasar da aka gudanar a Abuja babban birnin kasar.

Ya kuma tabbatar da cewa hukumomin sojin kasar sun karbi naria tiriliyan 2.5 a kasasfin kudi na shekaru bakwai da suka gabata, amma duk da haka sun yi kokarin inganta ayyukan harkokin tsaron cikin gida.

Sai dai kuma ya nuna nadama kan kudin da aka ware wa hukumomin sojin kasar, wanda ya ce kashi 35 ne cikin 100 na abin da hukumomin ke bukata.

Labarai Makamanta