Labarin dake shigo mana daga Birnin tarayya Abuja na bayyana cewar adadi mai yawa na ‘yan sanda cikin manyan motocin sintiri hudu ne suka mamaye hanyar shiga da fita a titin Blantyre da ke cikin sakatariyar jam’iyyar APC a Abuja.
An tattaro cewa a ranar Laraba ‘yan sandan da jami’an tsaro na DSS suna wurin ne domin dakile yiwuwar tabarbarewar doka da oda.
Wakilinmu ya samu labarin cewa jami’an tsaron sun taru ne bayan samun rahotannin tsaro game da shirin zanga-zangar da ‘yan APC suka shirya yi na nuna adawa da yadda jam’iyyar ta gudanar da zabuka a taronta na gangami na jihohi.
An hakaito cewa wasu ‘ya’yan jam’iyyar sun shirya gudanar da zanga-zangar adawa da Gwamna Mai Mala ne kan ci gaba da jagoranci kwamitin riko/tsare-tsare na musamman.
Da yake tsokaci kan lamarin, sakataren kwamitin rikon, Sen John Akpanudoedehe, ya shaidawa manema labarai cewa jami’an tsaro sun mamaye wurin ne bayan samun rahoton tsaro. A cewarsa:
“Babu wani abu da ke faruwa. Sun sha zuwa wurin a duk lokacin da muke bukatar kiyaye Sakatariyar.” “Ba ku da ikon karanta rahotannin tsaro, don haka ba za ku iya tambayata akai ba. Idan wani abu ya faru a yanzu, za su fadi me suke yi.
Akwai abubuwa da yawa da suka shafi tsaro da ba ku sani ba. “Abu ne na yau da kullum. ‘Yan sanda suna hulda da Ministan Abuja, Shugaban ‘yan sanda da sauran manyan mutane.
“Mun karanta rahotannin tsaro kuma na tabbata kun san cewa muna da kowace irin hukumar tsaro a sakatariyar mu. Muna aiki ne kawai da rahotannin tsaro, babu wani abin fargaba.”
You must log in to post a comment.