Rikici Ya Sake Sarkewa Tsakanin Wike Da Shugaban PDP

Labarin dake shigo mana daga birnin Fatakwal na jihar Ribas na bayyana cewar gwamnan jihar Wike ya wofintar da barazanar cewa za a kore shi daga babbar jam’iyyar adawa ta PDP.

Gwamnan ya bayyana cewa zai mayar da martanin da ya dace idan aka kore shi daga jam’iyyyar, inda zai jiĆ™a wa kowa aiki kowa ya gane kuren shi.

Gwamna Wike ya yi jawabi ne a taron da aka yi don karrama gwamnonin G5 a Fatakwal, jihar Ribasa a ranar Juma’a 18 ga watan Nuwamba.

Gwamnonin na G5 sun kunshi Seyi Makinde na Oyo, Samuel Ortom na Jihar Benue, Ifeanyi Ugwuanyi na jihar Enugu, Okezie Ikpeazu na jihar Abia da Wike kansa. Gwamnonin da suka yi wa jam’iyyar bore suna neman shugaban jam’iyyar na kasa Sanata Iyorchia Ayu ya yi murabus ne da sunan adalci da daidaito kafin su mara wa Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasar jam’iyyar baya.

“Sun ce za su kore ni. Ina jiran ranar da za su kore ni. Idan sun kore ni, zan barbada musu yaji, za su san cewa kaki ba leda bane.”

Labarai Makamanta