Rikici Ya Barke Tsakanin Hausawa Da Yarbawa A Legas

An Kulle Hanyar Legas Zuwa Abeokuta Biyo Bayan Rikicin Da Ya Barke Tsakanin Hausawa Da Yarbawa

Taho mu gama da ta faru tsakanin Yarbawa da Hausawa ‘Yan kasuwar Oke-Odo ya jawo kulle babbar hanyar da Legas zuwa Abeokuta.
Dukkanin motocin da suka nufi Legas daga Sango ta Jihar Ogun, da wadanda suke nufar Abule-Egba daga Oshodi da sauran sassan jihar sun tsaya cak babu motsawa.

Wani shaidar gani da ido ya bayyana cewar rikicin ya faro a jiya da dare, lokacin da ‘yan kasuwar ke hada hadar saye da saidawar kayayyakin abincin, sai rikicin ya tashi ba tare da sanin musabbabin shi ba.

Yanayin ya kazanta sosai a safiyar Lahadin nan, inda fusatattun matasan Yarbawa suka rinka banka wa shagunan ‘yan Arewa wuta ba tare da kakkautawa ba.

Related posts