Rigakafin Korona Ba Tilas Bane Ga ‘Yan Najeriya – Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewar yin allurar rigakafin korona ba zata zama tilas ba ga ‘yan Najeriya, sai dai bisa ganin dama akan haka gwamnatin za ta roki ‘yan kasa su amince ayi musu ita ne maimakon tilasta wa kowa ya yi allurar rigakafin Korona ta Oxford AstraZeneca wadda tuni aka fara yin ta a Najeriya.

Ƙaramin ministan lafiya Dr Olurunnibe Mamora ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a, a garin Asaba, yayin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai jim kadan bayan ya kaddamar da wasu ayyuka a Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya (FMC) dake Asaba babban birnin jihar Delta.

Bayanin nasa ya biyo bayan tambayar da wani dan jarida yayi ne kan dalilin da yasa har yanzu jihar Kogi bata karbi rabonta na allurar ba yayin da mafi yawan jihohin tarayya tuni sun karbi nasu kason.

Don haka, Mista Mamora ya yi sauri ya nuna cewa jihar Kogi ba a shirye ta ke ba da allurar rigakafin, yayin da Gwamnatin Tarayya kuwa ba za ta tilasta wa kowace jiha yin allurar ba.

“Kogi ba ta da wuraren ajiyar kayan sanyi, tsaro, kayan aiki da kuma ma’aikatan da za su yi allurar rigakafin.

“Har ila yau, bari in bayyana a sarari a nan cewa tun daga farko, Gwamnatin Tarayya ta bayyana karara cewa ba za ta tilasta wa kowa ya yi rigakafin ba, a maimakon haka za ta ci gaba da yin kira ga mutane su yi don radin kansu.

“Baya ga haka, jihar Kogi, da musamman ka ambata, daya daga cikin dalilan da ya sa ba a tura allurar can ba shi ne; saboda lokacin rikicin #EndSARS, an lalata wasu cibiyoyinsu da karfin tsiya.

“Don haka, yayin da muke magana, jihar Kogi ma ba ta da wuraren adanawa don kula da yanayin sanyi. Don haka, wannan shi ne dalilin da ya sa ba a samarwa jihar ba,” inji shi.

Ministan ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta ba da sharadi ga jihohi, don tabbatar da shirye-shiryen samar da kayan sanyi, kayan aiki, tsaro da ma’aikata don yin allurar rigakafin, kafin a samar da su.

Labarai Makamanta