Rigakafin CORONA Wajibi Ne Ga Dukkanin ‘Yan Najeriya – Fadar Shugaban Ƙasa


Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci dukkan ‘yan Najeriya da suka cancanta da su karbi allurar rigakafin COVID-19 domin kare kansu daga kamuwa da cutar.

Shugaban ya bayar da shawarar ne a ranar Asabar, 6 ga Maris, jim kadan bayan ya karbi kashi na farko na rigakafin korona na AstraZeneca, hadimin shugaban kasa, Garba Shehu ya bayyana a cikin wata sanarwa.

‘’Na karbi rigakafina na farko kuma ina so na yaba wa duk ‘yan Najeriya da suka cancanta, su yi hakan domin a kare mu daga cutar.

“Alurar rigakafin zai kare kasar daga cutar Coronavirus. Hakazalika ina kira ga duk ‘yan Najeriya da suka cancanta da su gabatar da kansu kuma a yi musu rigakafin bisa ga tsarin fifikon da aka riga aka tsara, a wasu cibiyoyin da aka ware kawai.”

Buhari ya roki dukkan gwamnatocin jihohi, sarakunan gargajiya da shugabannin addinai da su tattara mutane a kananan hukumominsu don yin rigakafin.

Ya yaba wa kamfanoni masu zaman kansu da masu ruwa da tsaki wadanda suka goyi bayan martanin Najeriya game da cutar.Buhari ya yi rigakafin ne da misalin karfe 11.51 na safe a wani takaitaccen bikin da manyan jami’an gwamnati suka halarta a dakin taro na New Banquet da ke Fadar Shugaban Kasa dake Abuja.

Babban likitan kansa, Dr Shuaib Rafindadi Sanusi ne ya yiwa shugaban kasar allurar ta rigakafin, yayin da mataimakin shugaban kuma Dr Nicholas Odifre, likita na musamman ga mataimakin shugaban kasar, in ji jaridar The Nation.

Labarai Makamanta