Rasuwar Mahaifiyar Yerima Babban Rashi Ne – Yahaya Bello

An bayyana rashin uwa a matsayin wani rashi babba a wajen iyali, inda duk wanda ya rasa mahaifiya ya yi rashi babba wanda babu irin shi ba, kuma ya cancanci tausayawa.

Mai girma Gwamnan Jihar Kogi Yahaya Bello ne ya bayyana hakan, lokacin da ya kawo ziyarar ta’aziya na rasuwar mahaifiyar Shugaban Ƙungiyar matasan Arewa Alhaji Yerima Shettima a gidan shi dake Kaduna.

Gwamna Bello ya kara da cewar babu wani mahaluki da zai iya maye gurbin mahaifiya a rayuwa saboda irin rawar da uwa ta taka wajen kula da ɗa har ya girma ya zama mutum, bisa ga haka duk wanda ya rasa wannan babban bango ya cancanci tausayawa.

Gwamnan wanda ya samu wakilcin Shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jihar Abdulkareem Jamiu, ya bukaci Shugaban matasan da sauran zuriyar marigayiyar da suyi koyi da kyawawan halayya na Mahaifiyar ta su sannan su dage wajen yi mata addu’o’i na samun rahama.

Da yake mayar da jawabi Shugaban Ƙungiyar Matasan na Arewa, ya godewa Gwamnan Jihar Kogi bisa ga ziyarar ta’aziya da ya kawo mishi, tare da alkawarin yin amfani da shawarwarin da Gwamnan ya bayar.

Labarai Makamanta