Rasuwar Attahiru Babban Rashi Ne A Ƙasa – Aisha Buhari


Uwar gidan shugaban Najeriya Aisha Buhari ta kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan Babban hafsan sojan Najeriya Janar Ibrahim Attahiru.

Aisha Buhari ta wallafa hotunan ziyarar ta’aziyar a shafinta na Twitter tare da saƙon ta’aziyya.

A ranar Asabar aka binne Babban Hafsan sojan tare da sojoji 10 da suka mutu a hatsarin jirgin sama a Kaduna.

Aisha Buhari ta ce rasuwar babban hafsan sojin babban rashi ne ga iyalansa da kuma Najeriya baki ɗaya.

Labarai Makamanta