Rashin Tsaro: Malaman Addini Na Daga Cikin Matsalolin Kasar Nan – Maqari

BASHIR ADAMU JALINGO

Babbban Limamin Masalancin Kasa dake Abuja, Farfesa Ibrahim Maqari yace Malamai, Yan-bani na iya na manyan Addinai a Najeriya na daga cikin wadanda suka jefa Kasannan cikin mummunar yanayin da take ciki a yau.

Shehin Malamin ya bayyana haka ne a wurin wani taron karawa juna sani na kwana daya da ‘Islamic Preachers Forum Taraba’ ta shiryawa Maluma masu Wa’azi a Birnin Jalingo, Fadar Jihar Taraba.

Da yake jawabi a wurin taron, Farfesa Ibrahim Maqari yayi Allah wadai da irin dabi’ar dabbanci da Al’ummah keyi, duk da karamah da Allah yayiwa dan-Adam.

Shehin Malamin na me cewa ya zama wajibi, masu wa’azi na manyan Addinai biyu a Kasannan su fahimci cewa tsaron Kasa hakkine daya rataya a wuyar kowa

“Allah Ya karrama Dan-Adam, amma a Yau Dan-Adam ya mayar da kanshi dabba mara daraja. Zamantakewa da Musulmai keyi a yau ba irin karantarwar da Manzon Allah ya karantar bane.

Farfesa ya cigaba da cewa ” Addinin Musulunci ya haramta cutar da Makwabci, koda kuwa wani irin Addini suke bi, ya zama wajibi Musulmai su kyautata alakarsu da abokanan zamansu wadanda ba Musulmai ba.

“Tabbas, Malamai ‘yan bani na iya na daga cikin awadanda suka jefa ‘Kasan nan cikin mummunar yanayin da take ciki a yau. Jihadi bawai kashe Mutane bane haka kawai, a’a zamantakewa mai kyau da alaka mai kyau kamr yadda Allah da Manzonsa ya sharrada ne babban Jihadi.

Ya kuma shawarci Gwamnatin Jihar Taraba, da tayi adalci a tsaknin Al’ummomin ta, da yin dukkanin mai yiyuwa da gaske ba na siysa ba, don kawo karshen rashin zaman lafiyar dake addaban Jihar.

A nashi bangaren, Limamin Masallacin Akpo Abuja, Sheikh Nuru Khalil, jadda-da nesanta kawarijawan Boko-Haram yayi da Musulunci.
“Yan ta’addan Boko-Haram ba wakiltan Musulunci sukeyi ba, ya zama wajibi su shaida hakan. “Kazalika, Mutanen Jihar Taraba yazama tilas a garesu su gujewa dukkanin masu ha’intansu domin cigaban kansu.

Reverend Solomon Kajingi shine Wakilin Kungiyar Kiristoci ta CAN, reshen Jihar Taraba a wurin taron, inda ya shawarci masu Wa’azi da suyi Wa’azi mai ma’ana dazai sa Al’ummah su tuba daga zunubansu, domin yin hakan zai kawo zaman lafiya a Kasa baki daya”.

Shugaban taro, Kur-Jibu na Bali, Abubakar Mahmud, da Babban bako mai Jawabi, Sarkin Ibi, Alh. Abubakar Yusuf Dan-Bawuro na biyu, sun nuna farin cikinsu tare da shawartan Malaman Addinan da suyi aiki tukuru wajen ganin an dawo da yarda da aminci a tsakanin maban-banta Addinai a Kasannan.

Hussaini Isma’il, shine Shugaban Kungiyar Islamic Preachers Forum a Jihar Taraba wanda ya shirya taron, ya jadda zaman lafiya tsakanin maban-banta akida a cikin Musulmai, da kawo karshen cin mutuncin da wasu Malamai keyiwa juna wurin wa’azi na daga cikin manufofin Kungiyar.

Kwamishinan Fasaha da Kimiyyya, Alhassan Hamman shine wanda ya wakilci Gwamnan Taraba yace taron bitar yazo dai-dai akan gaba, da manufofinshi na zaman lafiya, kuma cigaba bazai samu ba, sai da zaman lafiya, inda yayi alkawarin bada gudunmuwar Gwamnati dari bisa dari.

Labarai Makamanta